View Abstract

Title :

Hotancin Zuci a Wakar Sabo Wakilin Tauri ta Hamisu Sarkin Kidi

Authors :

Salisu Garba

Salo dai kamar yadda masana suka bayyana shi ne, dabaru da hikimomin jawo hankali domin isar da sako cikin sauki da burgewa ga mai saurare. Wannan ya sa fasihai kan yi kokarin darzo salon da zai taimaka musu wajen kama hankalin masu saurarensu domin samun damar cim ma muradinsu. A kokarin fasihai na cim ma wannan muradi nasu sukan sarrafa dubaru daban?daban, yayin da wasu ke kokarin dabbantar da mutane, wasu kuma su mutuntar da dabbobi, wasu kuwa su abuntar da su, wasu ma har salon jirwaye ko habaici suke sarrafawa. Wannan makala ta mayar da hankali ne wajen nazartar fitaccen salon nan na hotancin?zuci wanda Hamisu Sarkin Kidi Kano ya sarrafa a wakar Sabo Wakilin Tauri. Watau dabarar suranta wani ~oyayyen abu a cikin zukatan masu saurare ta yadda za su iya hararo shi da idanun zuciyoyinsu. Makalar ta nazarci yadda Hamisu Sarkin kidi ya dunkule manufofi masu tarin yawa ne a cikin kalmar arne tare da kokarin suranta wadannan ma'anoni a zukatan masu saurare. Makadin ya yi haka ne domin bayyanar da jarunta da bajintar gwaninsa a zukatan masu saurare. Daga karshe makalar ta gano yadda Hamisu Sarkin Kidi ya yi ta kokarin suranta jaruntar Sabo Wakilin Tauri, wadanda ya dunkule su a cikin kalmar arne da kuma yadda ya suranta kowace ma'ana faifai?faifai, ta hanyar kirkirar wata gwagwarmaya tare da danganta ta da Sabo Wakilin Tauri. Wani abin burgewan da makalar ta gano shi ne, kadaituwar Hamisu Sarkin kidi da irin wannan salo, iyaka sanin wannan makala, tamkar dai yadda Akilu Aliyu ya kadaita da wannan salo a marubuta wakoki.