View Abstract

Title :

Nazarin Kyau A Kyautayin Bahaushe Daga Wa}o}in Baka Na Hausa

Authors :

Abubakar Ayuba

Kyau a kyautayin Bahaushe wata irin nasaba ce tamkar ta jini da tsoka, kyau yana cike da }awa da kwarjini, rai yakan yi fari matu}ar ya sami abin da yake so ko kuma idan ya ga kyakkyawa. Kyau ko munin abu ya danganta ga abin da zuciyar mutun take so. Nagarta da halin kirki ]abi?u ne nagari, wa]anda jama?a suke maraba da su kuma suke martaba wanda ya aikata su. Wanda duk yake yin kyautayi, yana da kyakkyawan hali, yakan zama mai mutunci a idon mutane saboda juriyarsa ko gaskiyarsa ko kuma alherinsa da kirkinsa. A fuskar tasarifi, kyau shi ne tushen kyautayi, domin haka, kyau yana bayyana a nagarta duk da cewa kyautayi sa~anin kyau ne. Manufa, kyautayi ]abi?a ne, kyau kuma ba ]abi?a ba ne. Har-ila-yau, kwalliya tana da]a inganta kyau da }awata shi a idon mutane.