View Abstract

Title :

Hausar Masu kwallon kafa a Cikin Garin Sakkwato

Authors :

Muhammad M. Umar & Musa Shehu

Wannan bincike ya shafi karin harshen rukunin masu kwallon kafa a cikin garin Sakkwato. Wato binciken za a gudanar da shi ne don kokarin gano ainihin yanayin samuwar sauyi a sanadiyar zamantakewa, wanda ya haifar da Hausar masu sha?awar tamola. Domin tabbatar da samuwar wannan Hausar da ta sha bamban da ta wasu rukunan jama?a, za a yi amfani da kalmomi da sassan jimla, wa]anda suka fi armashi da kar~uwa a idon magoya bayan ?yan wasa ko kulob-kulob. Hanyoyin cim ma wannan }uduri sun ha]a da: Ziyarar kai tsaye a filayen buga }wallon }afa da kuma gidajen kallon }wallo daban-daban da ke a cikin garin Sakkwato, domin ji kai tsaye daga bakin masu amfani da wannan Hausar, da kuma samun damar tattaunawa da su, domin tattara bayanai. Haka kuma, binciken ya gano cewa masu harkar }wallon }afa sun }ware sosai wajen amfani da salon }ir}ira sababbin kalmomi, ta hanyar fa]a]a ma?anar kalmomin Hausa, da kuma Hausantar da kalmomin Ingilishi tare da sarrafa su ta yadda za su dace da tsarin Hausa mai mayar da ]an wani nata.