View Abstract

Title :

Huldar Soyayya Tsakanin Dan Adam Da ?Iska?-Aljani

Authors :

Yakubu Aliyu Gobir

Al?ummar Hausawa sun dade suna hul]a da iskoki. Tarihi ya nuna wannan hul]a ta samo asali ne tun lokacin da suke cikin addininsu na gargajiya. Bincike a kan addinin Bahaushe na gargajiya ya samu kar~uwa sosai ga masana al?adun Hausawa. A yau, goshin karni na ashirin da daya Hausawa sun bude wani sabon shafi na hulda da iskoki. A da, ?yan bori da bokaye da malaman tsibbu su ke cin karensu ba babbaka a kan sha?anin hul]a da iskoki. Yanzu an sami rukunin wasu malaman addini da suke hulda da iskoki ta hanyar rukiyya1, domin warkar da cututtukan da suka shafi iskoki. Daga cikin wadannan cututtukan da suka shafi iskoki akwai abin da Hausawa ke kira, ?Namijin Dare? ko ?Macen Dare?, wato hul]ar soyayya da ke gudana tsakanin Dan Adam da iskoki (Tsakanin mace mutum da aljani namji ko tsakanin aljana da mutum namiji). Gano yadda Hausawa ke warkar da wannan cutashi ne makasudin wannan makala.