View Abstract

Title :

ISA RASCO DANGOMA: AYYUKANSA A DUNIYAR ADABIN HAUSA

Authors :

Umar Aliyu Bunza

Aikin samar da rubutaccen adabin Hausa wata hikima ce da Allah ya ba wa]ansu mutane cikin bayinsa. Wasu cikin marubutan sun yi fice, an ji su har ana nazarin ayyukansu a ilmance wasu kuma ba su sami wannan gatancin ba. Isa Rasco Dangoma na cikin marubuta da ba a san da ayyukansu ba a fagen ilimi duk da yawan rubuce-rubucensa da ya fara daga shekarar 1994. Daga wannan shekarar zuwa yau, ya samar da wa}o}i da }agaggun labarai da fim masu yawa, amma ba a sami wani da ya yi nazari kan adabin nasa ba. Ba shakka, adabin nasa na bu}atar nazari domin a fito da hikimomin da ke ciki, ya kuma bi sahun takwarorinsa. Manufata a wannan ma}ala ita ce sharar fage a nazarin adabin Isa Rasco Dangoma.