View Abstract

Title :

Yabo a Bakin Zabiyar Fada

Authors :

Halima Kabir Daura,

Masu iya magana na cewa, ?Yaba kyauta tukwici?. Tukwicin da mawa}a ke yi wa jama?ar da suke ba su abin hannunsu shi ne ta hanyar ambato abubuwa na gari a cikin wa}o}insu ko kirari. A iya cewa Zabiyoyin Fada kamar takwarorinsu maza, ba su yi butulci ba, su ma suna okari wajen yabon saraki da shikashikan cim ma yabo, wa]anda suka ha]a da : ambaton tarihin asali ga sarauta, da ri}o da addini, da kyauta, da jaruntaka, da kuma iya mulki ko ri}e jama?a, kamar yadda Bello (1976), ya bayyana. Amfani da yabo a matsayin jigo, musamman a wa}oki da kirarin fada, ruwan dare ne, domin shi ke }ara wa saraki kwarjini da }ima, a idanun talakawansa da sauran jama?a, baya ga sa saraki tun}aho.Wannan mu}ala ta yi }o}arin bibiyar yabo a kirarin da Zabiyoyin Fada kan aiwatar a wasu fadojin }asar Hausa.