View Abstract

Title :

Tsiya Adon?Yan Tauri: Nazarin Ayukkan Qungiyoyin Banga Ga Tsaron Qasa A Wasu Sassan Adabin Hausa

Authors :

AbdulbasirAhmad Atuwo

Tauri lamari ne da ya kasance abu mai matsayi a qasar Hausa musamman ta la?akari da irin faxi-tashin da suke yi wajenqoqarin tabbatar da tsaro ga al?umarsu da kuma taimako na samar wa jama?a da magungunan gargajiya da suka shafi cututtuka da kuma na kariyar kai kamar su kas-kaifi da sagau da ba-sanyi da ba-duhu da sauransu ba don komai ba sai domin tsare kansu da kuma al?umma daga ba-zata tare da son nuna jaruntaka da shirin ko-ta -kwana ta hanyar kare al?ummarsu qasa baki xaya ta hanyoyi daban-daban da suke iyawa. ?Yan tauri da mawaqansu na da kalmomi da dama waxanda suke amfani da su wajen kambama kansu a wuraren farauta da bukukuwa irin nasu domin samun damar gwada magungunansu ko makamansu ko nuna buwayarsu da jaruntakarsu. Wannan muqala ta dubi yadda wasu sassan adabin Hausa suka nuna muhimmancin samun qungiyoyin sa - kai na tsaron al?umma ko qasakamarqungiyoyin Banga ko Tauri.daga cikin waxannan hanyoyi tare da nazarin irin yadda mawaqansu ke amfani da zavavvun kalmomi na tunzurawa domin kambama su domin su yi kwaxayin ba da ta su gudummawa wajen tabbatar da tsaro a cikin jama?arsu da kuma qasarsu baki xaya.Haka kuma muqalar ta dubi littafin ?Idon Matambayi? na Muhammadu Gwarzo da ?Shaihu Umar? na Abubakar Tafawa Valewa domin ganin irin yadda Marubuta suka fito da nason qungiyoyin sa ? kai na Banga domin kiyaye tsaron jama?ar qasa daga ?yan ta?adda. Wannan shi ya sa aka ba muqalarsuna ? Tsiya Adon ?Yan Tauri: NazarinAyukkan Qungiyoyin Banga Ga Ayukkan Tsaron Qasa A Wasu sassan Adabin Hausa.