View Abstract

Title :

Gabatar da Dabarun Nazarin Al?adun Al?umma a Cikin Hausa

Authors :

Nasiru Aminu

Lokaci mai tsawo, fagen al?ada ba shi da nasa ke~a~~un dabarun nazarin al?adun Hausawa a cikin harshen Hausa, ya dogara ne a kan hanyoyin nazari daga wasu fagage na Ilimi, kamar ilimin Walwalar Dan Adam (Sociology) da na tarihin al?adu (Anthropology) da ilimin labarin} asa (Geography), inda yake yin aro domin bincike da samun nasarar nazarce-nazarce, da koyar da al?ada. Wannan na nuni ga cewa, akwai} aranci da rashin mayar da hankali wajen samar da rubutattun litattafai a cikin Hausa masu bayani kan dabarun da manazarci Hausa zai iya amfani da su wajen nazarin al?adun Hausawa, ba tare da dogara a kan ba} on harshe ba. Haka, rashin tsayayyun hanyoyi da dabarun nazarin ilimin al?ada a cikin Hausa, ya sa malamai da] aliban al?ada rashin samun cikakkiyar fahimta da wata madafa kan yadda za su fuskanci bincike kan al?adun al?umma, wannan ne mafarin matsala ga sha?anin bincike da koyar da ilimin al?ada. Don haka manufar wannan ma} ala ita ce yin matashiya a kan dabarun nazarin al?ada a cikin Hausa, musamman don amfanin masu bincike da] aliban al?ada. Ma} alar ta yi matsayar cewa rashin ingantattun dabarun bincike a cikin harshen Hausa, wata matsala ce da ke hana samun ingantattun bayanai kan al?adun Hausawa na asali, kuma wannan na iya haifar da koma baya wajen koyar da al?adun Hausawa ga] aliban al?ada. Don haka wannan takarda ta kawo wasu dabaru da hanyoyin nazarin al?ada a cikin Hausa, da za su iya zama jagora ga masana da] aliban al?ada.