View Abstract

Title :

Nazari akan Nahawun Hausa na Taciya da Kirar Kalma a Takaice

Authors :

Isah Abdullahi Muhammad

Taken wannan takarda shi ne ?Mazhabar Nahawun Taciya Da Nazarin {irar Kalma A Hausa? A }arni na 19 zubi da tsarin nazarin nahawu a lokacin yana da matu}ar kama da nazarin }irar kalma a yau (Haspelmath 2002:1). Sannan hakan abin ya ci gaba har zuwa }arni na 20. Kwatsam! Bayan nahawun tsirau ya mamaye duniyar nazarin harshe, sai batun ya sauya (daga 1950-1969) kwata-kwata aka jingina zancen }irar kalma. Sai aka kuma, rarraba bayanansa zuwa ~angaren tsarin sauti da ginin jumla. Sai a shekarar 1970 Chomsky a fitacciyar ma}alarsa mai taken ?Remarks On Nominalization?, ta sake dawowa da fagen }irar kalma a nazarin kimiyyar harshe. Wannan ma}ala (ta Chomsky 1970), ta haifar da muhawarori wa]anda har yanzu ba a warware su ba. Daga ciki wa]annan batutuwa akwai: Kasancewar fagen }irar kalma a matsayin ?yantaccen fage mai cin gashin kansa. Sai kuma, farfajiyar nazarin }irar kalma ?kalma?. Sai zancen tubalin nazarin }irar kalma wato ?}wayar kalma?. Akwai kuma, batun bambancin a tsakainin kumbura da tsira. Sai zancen ha}i}anin iyaka da kuma ala}a ta fagen nazarin }irar kalma da sauran ~angarorin nazarin nahawu wanda shi ake kira ?Gamayyar }irar kalma? da sauransu. Malaman }irar kalma suna amfani da misalai daga harsuna daban-daban wajen bayyana matsayarsu a kan batutuwan. Wannan muhawara, ta }ara fa]a]a fagen nazarin }irar kalma. A nan kuma, za a kawo misalai daga Hausa don tattauna wa]annan batutuwa.