View Abstract

Title :

Kwatancen Aladun Bikin Ra?in Sunan Jariri Tsakanin Hausawa Da Misirawa

Authors :

Abdulrahman Ado

Dangantaka a tsakanin Hausawa da Misirawa daxaxxiya ce. Al?ummu guda biyu sun daxe da samun cuxanya da juna ta fannoni da yawa, irin su ilimi da kasuwanci da ziyara da auratayya da makamantansu da yawa. A sanadiyyar wannan dangantaka, an sami cuxanya da juna wadda ta haddasar da samuwar watsuwar al?adun Misirawa zuwa cikin al?ummar Hausawa. Yawan al?adun da Hausawa suka ara daga Misirawa ya sanya wasu masana da manazarta suka yi hasashen cewa Hausawa suna da tushen asali xaya da Misirawa. A wannan nazari, an duba wasu kamanci da bambancin da ke akwai, na al'adun bikin ra?in suna, tsakanin Hausawa da Misirawa domin yin qoqarin laluben dangantakar Hausawa da Misirawa ta asali da cuxanya da juna. A cikin takardar an yi qoqarin kawo kamanci da bambancin hidimomin da al?umman guda biyu suke aikatawa na al?adar yinin bikin suna, tun daga wayewar gari, wato farkon fara shi, har zuwa lokacin gama shi, da yamma ko da dare. Kazalika, an kawo bayani na ra?in da aka xora binciken a kai da kuma waiwayen wasu ayyuka da aka yi masu alaqa da wannan bincike domin tabbatar da cewa babu wani bincike da aka tava gudanarwa irin wannan.